Guinea : An Rantsar Da Shugaba Conde A Wa’adin Mulki Na Uku

2020-12-15 22:09:04
Guinea : An Rantsar Da Shugaba Conde A Wa’adin Mulki Na Uku

Shugaba Alpha Conde, na Guinea, ya yi rantsuwar kama aiki a wa’adin mulki karo na uku mai cike da kace nace a wannan Talata.

Shugaban mai shekaru 82, ya sha rantsuwa ne a gaban kotun tsarin mulkin kasar, a bikin da aka shirya tare da halartar shuwagannin kasashen Afrika 11.

An gudanar da bikin ne a cikin tsauraren matakai na tsaro, inda aka zuba ‘yan sanda da jami’an jandarma da kuma sojoji.

Shugaba Conde, dai ya samu damar tsayawa takara ne a karo na uku,bayan kwaskware kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar mika shi a zaben raba gardama.

‘yan adawa na kasar dai sun kauracewa zaben, wanda ya bashi damar sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na ranar 18 watan Oktoba da ya gabata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!