Tunusia Ta Ce Ba Ta Shirya Kulla Alaka Da Isra’ila Ba

2020-12-15 22:06:54
Tunusia Ta Ce Ba Ta Shirya Kulla Alaka Da Isra’ila Ba

Gwamnatin Tunusia, ta bayyana cewa kulla alaka da Isra’ila ba ya a gaban ta a halin yanzu.

Da yake sanar da haka a wata hira da gidan talabijin na F24, firaministan Tunusiar, Hichem Mechichi, ya ce daidaita alaka tsakanin kasarsa da Isra’ila ba batu ne dake cikin ajandar kasar ba a yanzu.

firucin na Tunusia na zuwa ne kwanaki kadan bayan da makobciyarta Morocco ta sanar da dawo da alakarta da Isra’ila.

Tunisia, ta kuma ce tana mutunta zabin kasar ta Morocco, a matsayin ta kasa ‘yar uwa.

Ko wacce kasa na da nata zabi, da kuma yadda take tafiyarda diflomatsiyyarta, wacce za ta amfane ta da al’ummarta, inji firaministan na Tunusia.

A ranar Alhamis data gabata ce shugaba Donald Trump na AMurka mai barin gado, ya sanar dawo da alaka tsakanin Isra’ila da Morocco, a yayin da ita kuwa Amurkar ta amince da ikon kasar ta Morocco akan yankin Saharaoui.

Yanzu dai Morocco, ta zama kasar larabawa ta hudu data amince da kulla alaka da Isra’ila a kasa da wata shida, bayan H.D Larabwa, Bahrain da kuma Sudan.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!