Pogba Ya Ce Yana Nan A Kungiyarsa Ta Manchester United

2020-12-15 21:00:39
Pogba Ya Ce Yana Nan A Kungiyarsa Ta Manchester United

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba, ya bayyana cewa bai kamata a ci gaba da tattaunawa a kan maganar makomarsa ba a halin yanzu, saboda haka zai ci gaba da dagewa yana sadaukarwa a kungiyar tasa.

Jaridar Leadership ta bayar da rahoton cewa, a makon daya gabata ne wakilin dan wasa Pogba kuma mai kula da harkokin wasanninsa, Mino Rioala ya bayyana cewa Pogba ba ya jin dadin wasa a Manchester United ya kamata ya sauya kungiya a watan Janairu

A watan Yunin shekara ta 2022 kwantiragin dan wasan tawagar Faransa zai kare, zai kuma iya barin Old Trafford a watan Janairun shekara ta 2022 a matakin wanda bai da yarjejeniya kuma Pogba, mai shekara 27, ya buga wasanni tara a gasar Premier League har da biyar da a ka fara bugawa da shi a fili a kakar bana.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!