A kalla Mutane 27 Ne ‘Yan Boko Haram Su Ka KAshe A Yankin Diffa Na Jamhuriyar Nijar

2020-12-15 14:57:40
A kalla Mutane 27 Ne ‘Yan Boko Haram Su Ka KAshe A Yankin Diffa Na Jamhuriyar Nijar

Majiya tsaro ta yankin na Diffa ta shaida wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa; A kalla mutane 27 ne su ka rasa rayukansu a daren Asabar, wayewar safiyar Lahadi a sanadiyyar wani mummunan hari da Boko Haram ta kai.

Majiyar ta ce kungiyar ta Bokoharam ta kai harin ne sa’o’i kadan gabanin a bude zaben kananan hukumomi a fadin kasar da ya hada da wani sashe na yankin Diffa.

Harin, an kai shi ne a kauyen Toumour a karkashin gundumar Diffa da ke kusa da iyaka da Nigeria.

Babban jami’in zabe a yankin ya ce maharan sun rushe kauyen da kaso 60%.

Yankin na Diffa yana cikin inda kuniyar ta Bkoharam ta fi tsananta kai hare-hare a jamhuriyar Nijar.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!