Alummar Iran Na da Hakkin Karya Takunkumi Kuma Ta Sayar Da Manfetur Dinta

2020-12-15 11:51:08
Alummar Iran  Na da Hakkin Karya Takunkumi Kuma Ta Sayar Da Manfetur Dinta

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani a lokacin da yake taron manema labarai na ciki da wajen kasar a jiya litinin ya jaddada hakkin alummar Iran na karya duk wani takunkumi da aka kakaba mata da kuma siyar da manfetur din kasar ga kasashen duniya, kuma ana tsammanin samun wani canji a yanayin da ake ciki a nan gaba bayan zuwan sabuwar gwamnatin Amurka.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa game da yiwuwar Amurka ta koma teburin tattaunawa kan shirin nukiliya Iran, ya fadi cewa kasar Amurka ta dade tana jawo wa Iran asarori masu yawa a tsawon shekaru, don haka lamarin bai takaita da janyewar da ta yi a yarjejeniyar da aka cimma kan nukiliyar kasar ba, wannan yana koma wa ne tun shekata 1957 zuwa yau.

Ya kara da cewa a yalin yanzu ba zai iya ba da wani tabbaci akan wannan ba, domin al’amari ne da ya shafi yadda dukkan bangarorin da ake tattaunawa da su suka yi aiki da alkawuran da suka dauka, duk lokacin da gungun kasahen turai biyar game da kasar Jamus suka yi aiki da alkawuransu to ita ma Iran za ta aiwatar da dukkan alkawuran da ta dauka nan take.

Daga karshe ya nuan cewa Iran ba za ta amince da duk wani sharadi game da yarjejeniyar da aka cimma kan shirin ta na nukliya ba , tana bukatar a aiwatar da dukkan abubuwan da aka cimma matsaya akansu ne daga kowanne bangare ba ba daga bangare daya ba.

013

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!