Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Kira Da A Saki Dukkan Daliban Makarantar Sakandire Ta Garin Kankara Da Gaggawa
2020-12-15 11:48:47

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ne ya yi wannan kira ne a cikin wata takarda da kakakinsa Staphene Dujarric ya fitar a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Ina kira da a gaggauta kwato daruruwan daliban makarantar Sakandiren gwamnatin ta kimiyya da ke garin kankara a jihar Katsina da yan bindiga suka sace su.
A wani
bangare kuma Ita ma hukumar Unicef mai
kula da kananan yara dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, cikin wata takarda
da daraktanta dake kula da Afirka ta yamma da ta tsakiya Marie-pierre ta fitar a
ciki, ta taya ilahirin iyayen wadannan
dalibai bakin cikin abin da ya faru na sace musu yaya da yan bindiga suka yi , da irin mawuyacin halin
da suka tsinci kansu a ciki sakamakon afkuwar wannan bala’i.
Haka zalika ta yi kira da a gaggauta ceto wadannan yaran da ba su dauki alhakin kowa ba, tace ya kamata yara kananan su kasance a wuri da ke da tsaro da za su samu tabbaci da natsuwa na kare rayuwakansu ba tare da fuskantar wata barazana ba.
013
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!