An Rantsar Da Allasane Ouattara A Matsayin Shugaban Kasar Ivory Coast A Karo Na 3

Bikin rantsuwar kama aikin din da aka gudanar ya samu halartar shuwagabannin kasashen Afrika guda 13 da kuma tsohon shugaban kasar Faransa Nikolas Sarkozi.
Shugaban
kasar dan shekaru 78 da haihuwa ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na 3
ne a zaben da aka gudanar a ranar 31 ga watan Oktoba da ya gabata da gagarumar
nasara.
Jami’iyun adawa
a kasar sun bayyana cewa tsayawa takarar a karo na 3 ya sabama kundin tsarin
mulkin kasar. Wannan ya sa ya fuskanci turjiya da nuna rashin amincewa daga
bangaren yan adawan.
Sai dai
shugaban kasar da magoya bayansa sun musanta wannan zargin, inda suka nuna cewa
kwaskwarima da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar a shekara ta 2016 ta ba wa
shugaban kasar damar sake tsayawa takara a karo na 3.
Tuni dai aka cafke mafiyawancin shuwagabannin
yan adawa a kasar kuma an dauki matakin
sharia kan zargin da ake musu da kokarin ta da fitina a kasar.
Rikice-rikicen da aka yi na kafin da bayan
zaben ya lashe rayukan mutane 85.
013