Najeriya: Ana Daukar Matakai Domin Ceto Daliban Da Ke Hannun ‘Yan Bindiga – Masari

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello
Masari ya bayyana cewa, hadin gwiwar jami’an tsaro na ci gaba da daukar
dukkanin matakan da suka dace, domin ganin an ceto daliban da suke a hannun ‘yan
bindiga.
Gwamna Masari ya bayyana cewa, ya
zuwa yanzu dai dalibai sama da 300 ne ake da tabbacin suna hannun ‘yan
bindigar, bayan sama da dari biyar sun dawo, daga cikin dalibai 884 da suke a
cikin makarantar sakandare ta Kankara a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari a
cikinta daren Juma’a.
Ya ce ko shakka babu abin da ya faru
abu ne mai matukar tayar da hankali, amma ya bayar da tabbacin cewa ba za su yi
kasa a gwiwa ba har sai sun tabbatar da cewa an bi dukkanin hanyoyin da
wadannan dalibai za su dawo ga iyayensu lami lafiya.
Wata tawagar gwamnatin tarayya
karkashin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Babagana Monguno ta
ziyarci jihar ta Katsina, domin jajantawa gwamnan da sauran wadanda abin ya
rutsa da su, inda Monguno ya bayar da tabbacin cewa suna bin kadun lamarin ‘yan
bindigar da kuma daliban da suka sace, kuam suna daukar matakai kan hakan.
Yanzu haka dai shugaba Buhari yana
cikin jihar ta katsina inda yake hutu a garin Daura, duk da cewa har yanzu bai
ziyarci garin na Kankanra domin ganewa idanunsa abin da ke faruwa ba, amma mai
magana da yawunsa Garba Shehu ya ce shugaba Buhari ya kadu da jin labarin abin da
ya faru, ya kuma yi Allawadai da hakan.
Haka nan kuma kakin an shugaba Buhari, Garba Shehu ya ce; dalibai 10 ne kawai ‘yan bindigar suke rike da su, sabanin abin da jami’an tsaro da kuma gwamnatin jihar Katsina ta fada, inda ta tabbatar da cewa dalibai 333 ne suke a hannun ‘yan bindigar.
015