​MDD: Mutane Kimanin Biliyan Biyu Za Su Iya Kamuwa Da Corona A Duniya

2020-12-14 21:15:09
​MDD: Mutane Kimanin Biliyan Biyu Za Su Iya Kamuwa Da Corona A Duniya

Wani rahoton hukumomin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, akwai yiwuwar mutane biliyan 2 za su iya kamuwa da cutar Corona da ma wasu cututtukan na daban a duniya.

Rahotan na hadin gwiwa da Hukumar Lafiya da Hukumar UNICEF suka rubuta ya ce aiki a cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da samun ruwa, da tsaftataccen wurin aiki ba, da tura likitoci ko masu taimaka musu, ba tare da ba su kayayyakin da zasu kare kansu ba, lamari ne mai matukar hadari.

Babban daraktan Hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Gebreyesus ya bayyana samar da ruwa da tsafta a cibiyoyin kiwon lafiyar a matsayin ginshikin dakile cutar korona a duniya.

A cewar Rahoton,a cikin dukkanin cibiyoyon kiwon lafiya hudu a duniya, uku ba su da ruwan da ake bukata domin tsaftacce dukkanin abubuwan da suke bukatar tsafka a cikin irin wannan yanayi, wanda kuma hakan yafi yawa ne a cikin kasashe masu tasowa.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!