​Ronaldo Ya Kafa Tarihi Na Lashe Manyan wasanni 400 A Nahiyar Turai

2020-12-14 20:15:38
​Ronaldo Ya Kafa Tarihi Na Lashe Manyan wasanni 400 A Nahiyar Turai

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a jiya na samun nasarar lashe manyan wasanni 400 a nahiyar turai, wanda babu wani dan wasa da ya taba samun wannan nasara a tarihin kwallon kafa.

Ronaldo dan shekaru 35 a duniya, ya taka gagarumar rawa a wasan da Juventus ta buga da Genoa, inda ya saka kwalle biyu da suka taimaka ma Juventus wajen samun nasara 3 – 1 a wannan wasa.

Dukkan kwallayen da Ronaldo ya ci sun zo ne daga bugun daga kai sai mai tsaron raga a cikin mintina 12 na karshen karawar, bayan da Stefano Sturaro ya farke kwallon da Paulo Dybala ya ci a farkon wasan.

Yanzu haka dai Ronaldo ya buga wa Juventus wasanni 100 kuma ya zura kwalle 77 a cikin wadannan wasanni.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!