Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kira Yi Wasu Jakadun Kasashen Turai Saboda Goyon Bayan Dan Leken Asirin Da Aka Zartarwa Hukuncin Kisa
2020-12-14 10:10:44

A jiya Lahadi Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Jamus domin nuna masa rashin yardarta da matsayar kasarsa da kuma tarayyar turai akan zartar da hukuncin kisan da aka yi wa Ruhullah Zam anan Iran.
Jakadan na kasar Jamus
Hans-Udo Muzel ya amsa sammacin na Iran akan tsoma bakin tarayyar turai din a cikin batun zartar da hukuncin kisa akan
Ibrahim Zam.
Har ila
yau, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta gayyaci jakadan kasar Faransa
Philippe Thiebaud shi ma akan matsayar kasarsa.
Jakadan ya yi alkawalin isar wa da gwammnatin kasar tasa sakon da aka ba shi.
Iran ta
zartar da hukuncin kisa ne akan Ruhullah Zam wanda aka samu da laifin ingiza
mutane domin tayar da hargitsi ta hanyar watsa labarun karya ta kafar Instegram.
013
Tags:
ma’aikatar harkokin wajen iran
ta kira yi wasu jakadun kasashen turai
ukuncin kisan da aka yi wa ruhullah zam anan iran
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!