Adadin Wadanda Covid-19 Ta Kashe A Amurka Sun Karaci Dubu 300

2020-12-14 09:57:57
Adadin Wadanda Covid-19 Ta Kashe A Amurka Sun Karaci Dubu 300

Adadin Wadanda Covid-19 Ta Kashe A Amurka Sun Karaci Dubu 300

Cibiyar tarayyar Amurka mai kokarin dakile cutuka masu yaduwa corona ta sanar da cewa ya zuwa yanzu wadand cutar ta kashe a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata sun kai dubu 2.3, yayin da wadanda su ka kamu da ita a wannan lokacin sun haura dubu 213.

Cibiyar ta Amurka mai kokarin dakile cutar ta corona ta kuma bayyana cewa; A cikin kwanakin bayan nan an sami karuwar masu kamuwa da cutar da kuma masu mutuwa.

A nata gefen, jami’ar John Hupkin mai bibiyar yaduwar cutar a cikin gida da duniya, ta bayyana cewa; A ranar Asbar din da ta gabata wadanda su ka mutu daga cutar sun kai 2,368,wadanda su ka kamu da ita kuwa sun kai miliyan 2, da dubu dari 195, da 10.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!