​An Gudanar Da Taro Domin Tunawa Da Abin Da Ya Faru Zaria A 2015

2020-12-13 22:46:55
​An Gudanar Da Taro Domin Tunawa Da Abin Da Ya Faru Zaria A 2015

Taron wanda ya gudana a jiya a birnin Qom na kasar Iran ya samu halartar manyan malamai da masana da kuma wasu daga cikin dalibai ‘yan Afirka da ma na wasu kasashe da suke zaune a birnin.

Daga cikin wadanda suka gabatar da bayanai akwai shugaban cibiyar Hauza Ayatollah Aarafi, da kuma shugaban cibiyar Majma’a ta Ahlul bait (AS) ta duniya, gami da wasu daga cikin manyan baki.

Baya ga haka kuma diyar Sheikh Zakzaky Suhaila Zakzaky ta gabatar da nata jawabin, inda ta yi bayani a takaice kana bin da ya farua Zaria a lokacin farmakin jami’an soji, da kuma yadda aka kashe ‘yan uwanta da kuma sauran magoya bayan Harka Islamiyya masu yawa, wadanda majiyoyin harka suke bayyana adadinsu da cewa yah aura mutane 1000.

Kuma a lokacin ne aka kama mahaifinta Sheikh Ibrahim Zakzaky da mahaifiyarta malama Zinat Ibrahim wadanda har yanzu ake ci gaba da tsare su a kurkukun Kaduna.

Taron ya kirayi gwamnatin Najeriya da hakan ya hada da shugaban kasa da ‘yan majalisa da sauran bangarorin na Shari’a da su bayar da hadin aki domin ganin an kawo karshen wannan batu na ci gaba da tsare Sheikh zakzaky.

Kamar yadda kuma taron ya jaddada cewa akwai kyakkyawar alaka tsakanin Iran da Najeriya, domin kuwa suna da jakadu a kasashensu kuam suna tafiyar da dukkanin harkokinsu na diflomasiyya lami lafiya, a kan haka taron ya bukaci ganin an warware wannan matsala, da kuam sakin sheikh Zakzaky da mai dakinsa da ake tsare da su.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!