Iran : An Karrama Shahid Fakhrizadeh Da Lambar Yabo Ta Martaba Sojoji

2020-12-13 21:27:38
Iran : An Karrama Shahid Fakhrizadeh Da Lambar Yabo Ta Martaba Sojoji

Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran, Ayyatollah Sayyid Ali Khamenei, ya karrama masanin nukiliyar nan na kasar Shahid Mohsen Fakhrizadeh, da lambar yabo ta martaba sojoji.

Da yake mikawa iyalin shahidin lambar, babban hafsan hafsohin sojin kasar Iran, Janar Mohammad Baqeri, ya bayyana lambar yabon a masatyin wacce ake martaba ‘yan kasa wadanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare juyin juya halin musulinci da hurimi da kuma ‘yancin kasar.

Haka kuma a cewar Janar Baqeri, lambar yabon it ace mafi girma da ake martaba wadanda sukayi hidima wajen samar da ci gaban kasar ta fuskar kayan soji da na’urori.

Masanin nukiliyar kasar ta Iran, Fakhrizadeh, ya yi shahada ne a ranar 27 ga watan Nuwamba da ya gabata sakamakon wani hari da aka kaiwa tawagar motocinsa a kusa da birnin Tehran.

Iran dai na mai zargin Isra’ila, da kai harin wanda ta ce an yi amfani da bindigogi wadanda aka sarafa da tauraren dan adam, saidai har yanzu Isra’ila bata ce uffan ba kan batun.

Iran dai ta sha alwashin maida martani a lokacin da ya dace.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!