Ana Zaben Wakillan Jihohi Da Na Kananan Hukumomi A Nijar

2020-12-13 20:22:28
Ana Zaben Wakillan Jihohi Da Na Kananan Hukumomi A Nijar

A Jamhuriyar Nijar, kimanin ‘yan kasar miliyan 7 da rabi ne ake kyautata zaton sun kada kuri’a a zaben wakillan kananan hukumomi dana jihohi a yau Lahadi, gabanin babban zaben kasar na ranar 27 ga watan Disamban nan.

‘Yan kasar dai zasu zabi wakillansu a cikin kananan hukumomi 266 na kasar, a tagwayen zabubukan da aka sha dagewa tun daga shekara 2016.

Rahotanni daga kasar sun ce zaben ya gudana cikin lumana saidai an samu tsaiko wajen bude wasu runfukan zabe, sannan kuma ba’a kiyaye matakan yaki da cutar korona ba.

Kafin hakan dai Hukumar zaben kasar ta CENI, ta ce ba’a samu yin rejistar zaben jama’a ma a wasu sassan kasar dake fama da hare haren mayakan dake ikirari da sunan jihadi musamman a yankunan yammaci da kudu maso gabashin kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!