ICC Za Ta Binciki Laifufukan Boko Haram Da Sojoji A Najeriya
2020-12-13 18:43:34

Babbar mai shigar da kara ta kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, Fatou Bensouda, ta sanar da cewa kotun ta ICC, ta cimma matsaya game da shirin kaddamar da bincike game da wasu munanen laifuka a Najeriya.
Binciken zai maida hankali ne kan kungiyar nan ta boko haram da kuma gwamnatin tarayya Najeriya.
Jami’ar ta shaida cewan komi ya kammala a matakin farko domin gudnar da bincike game da halin da ake ciki Najeriya, game da kungiyar ‘yan ta’adda ta boko haram da kuma sojojin Najeriya.
Kotun
ta ICC, ta ce ta samu bayanai kwarara dake
tabbatar da cewa mambobin kungiyar boko haram da sojojin gwamnatin Najeriya sun
aikata laifukan yaki da cin zarafin bil adama.
024
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!