A Karon Farko An Fara Kai Kayan Agaji Zuwa Yankin Tigray Na Kasar Habasha

2020-12-13 14:36:18
A Karon Farko An Fara Kai Kayan Agaji Zuwa Yankin Tigray Na Kasar Habasha

A jiya Asabar ne dai agajin daya daga cikin kungiyoyin kasa da kasa ya isa yankin na Tigray wanda shi ne karon farko tun barkewar rikici kusan wata daya da ya gabata.

Kungiyar agaji ta “Red Cross” ta sanar da aikewa da magunguna da sauran kayan aikin likitanci a cikin manyan motoci bakwai saboda a taimakawa mutanen da adadinsu ya kai 400 da su ka jikkata a birnin Mekele.

Shugaban kungiyar ta agaji a nahiyar Afirka Patric Yossef, ya ce magungunan da aka aike za su taimaka matuka wajen aikin da likitoci su ke yin a ceton rayuka a cikin birnin na Mekele.

Gwamnatin Habasha dai ta dauki tsauraran matakai na shiga cikin birnin Mekele tun da rikici ya barke.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!