Mutane Biyu Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Wani Bom A Birnin Kabul Na Afghnanistan Da Safiyar Yau Lahadi

2020-12-13 14:32:34
Mutane Biyu Sun Mutu Sanadiyyar Tashin Wani Bom A Birnin Kabul Na Afghnanistan Da Safiyar Yau Lahadi

Da safiyar yau Lahadi ne wani bom ya tashi a birnin Kabul, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu da kuma jikkata wasu biyu.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan birnin Kabul Firdaus Faramarz ya tabbatarwa da manema labaru tashin bom din da kuma asarar rayukan da ya haddasa.

An kai harin ne dai akan wata motar “Land Cruizer” da ke a bakin Hotel din Parvan, a gunduma ta 15 a cikin birnin na Kabul.

Wata majiyar ta ambaci cewa harin yayi sanadiyyar kashe mai matukin mota da mai gadi na dan Majalisar dokokin kasar ta Afghanistan mai suna; Taufin Wahdat.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya wacce ta dauki alhakin kai wannan harin.

A jiya Asabar ma an kai wa birnin na Kabul hari da makamin roka wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu hudu.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!