Sojojin HKI Sun Kutsa Cikin Gidajen Palasdinawa A Daren Jiya A Yammacin Kogin Jordan

2020-12-13 14:28:46
Sojojin HKI Sun Kutsa Cikin Gidajen Palasdinawa A Daren Jiya A Yammacin Kogin Jordan

A yayin kutsen na sojojin Sahayoniya a cikin garuruwa daban-daban na yammacin kogin Jordan, sun yi awon gaba da samarin Palasdinawa.

A cikin birnin Kudus kadai ‘yan sahayoniyar sun kame samari uku a yankin al-wad, ba tare da wani dalili ba, haka nan kuma wani saurayi guda a kusa kofar Asbat da ke jikin masallacin Kudus.

Har ila yau, ‘yan sahayoniyar sun yanke hukuncin korar Ahmad Abu Gazala al-makdasy daga masallacin Kudus har tsawon watanni uku masu zuwa.

A cikin garin Al-Isawiyyah mai makwabtaka ta birnin kudus, an yi tawo mu gama a tsakanin samari da kuma sojojin mamayar da su ka yi amfani da harsashen roba.

A garin Bethlaham ma, sojojin mamayar sun yi kutse a cikin yankin Jabal-Ummu Rakbah inda suka tsare hanyoyin na sa’o’i da dama.

Daga lokaci zuwa lokaci, sojoji da ‘yan sandar HKI sukan kutsa cikin garuruwa da biranen Palasdinawa inda su ke kame Palasdinawa ba tare da wani dalili ba.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!