Ministan Harkokin Wajen Kasar Turkiya Ya ce Kasarsa Tana Mutunta Hurumin Kasar Iran

2020-12-13 10:22:29
 Ministan Harkokin Wajen Kasar Turkiya Ya ce Kasarsa Tana Mutunta  Hurumin Kasar Iran

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Turkiya Mevlut Cavusuglu ya yi da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya bada tabbacin cewa shugaban kasar Rajab Dayyib Ardigan yana mutunta karfin ikon jamhuriyar musulunci ta Iran da kuma matsayin da kasar take da shi.

Har ila yau ya jaddada game da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna , kuma game da wakar da shugaban kasar ya karanta da ya nemi kawo tarnaki a alakar da ke tsakanin kasashen biyu ya ce shugaban ya karanta wakar ce a garin Baku domin bai san yanayin dake tattare da ita ba, kuma ya danganta ta ne da Lachin da kuma Karabakh.

A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar Iran shi ma ya jadda game da irin abokanta ta kud da kud da ke tsakanin kasashen biyu kana ya yi fatan samun ci gaba sosai game da dangantakar dake tsakaninsu ta hanyar mutunta juna.

A ranar juma’a da ta gabata ne kasar Iran ta kira yi jakadan Turkiya a kasar domin nuna rashin jin dadinta game da wata waka da shugaban kasar na turkiya ya yi da ke taba martabar kasar Iran da alummarta.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!