Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Kai Ziyara Kasar Afghanistan

2020-12-13 10:16:55
 Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Kai Ziyara  Kasar Afghanistan

Rahotannin sun bayyana cewa mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran Sayyid Abbas Araqchi ya kai ziyara birnin Kabul ne domin tattaunawa da manyan jami’an gwamnatin kasar , da nufin kammala cikakkaun bayanan dabarun hadin guiwa tsakanin kasashen biyu.

Masana sun yi amannar cewa wannan ziyarar za ta kara karfafa dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.

A wata hira da gidan talbijin din Pres TV ya yi da mataimakin ministan ya fadi cewa jami’an kasar Iran sun jaddada game da muhimmacin kara karfafa dangantaka tsakanin Tehran da Kabul ta hanyoyi daban- daban.

Wannan ziyara ta zo ne a daidai lokacin da kasashen biyu suka bude jirgin kasa na hadin guiwa da zai hade Yammacin kasar Afghanistan da kuma Gabashin kasar Iran da hakan yake tabbatar da samun karin kyakkawar dangantaka da yin aiki tare tsakanin kasashen biyu.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!