Zainudden Zidane Ya Shirya Barin Kungiyar Kwallon Kafa Ta Real Madrid
2020-12-13 10:04:07

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zidane ya sanar da aniyarsa ta barin kungiyar a karshen kakar bana, saboda irin yanayin da kungiyar take ciki na rashin tabbas in ji shi.
Shi dai Zidane ya bukaci hukumomin
kungiyar kwallon kafar ta Real Madrid ne da su dauko masa wasu sabbin yan wasa
kamar Paul Pogba na Manchester United da
Sadio Mane na Liverpool , amma suka yi kunnen uwar shegu da bukatun nasa suka bar
shi da yan wasan da basa iya buga wasa yadda ya kamata.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa shugaban gudanarwa na kungiyar ta Real Madrid daga baya ya lallashi kocin inda ya sha alwashin siyo ‘yan wasan da yake bukata a karshen kakar kwallon kafa ta bana, sai dai babu tabbas ko idan za su iya sayan yan wasan da shi yake bukata.
Tags:
zainudden zidane
ya shirya barin kungiyar kwallon kafa ta real madr
paul pogba na manchester united
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!