​Gharib Abadi: Ya Kamata Hukumar IAEA Ta Zama Mai Cikakken ‘Yanci A Cikin Ayyukanta

2020-12-12 20:17:58
​Gharib Abadi: Ya Kamata Hukumar IAEA Ta Zama Mai Cikakken ‘Yanci A Cikin Ayyukanta

Wakilin Iran a ofishin harkokin kasa da kasa da ke birnin Vienna na kasar Austria ya bayyana cewa, ya kamata hukumar makamshin nukiliya ta duniya ta zama mai cikakken ‘yanci.

A cikin wani bayani da ya fitar a yau, dangane da halin da ake ciki kan batun ayyukan hadin gwiwa da ke tsakanin Iran da hukumar IAEA, wakilin Iran a ofishin harkokin kasa da kasa da ke birnin Vienna na kasar Austria Kazem Gharib Abadi ya bayyana cewa, ya kamata hukumar makamshin nukiliya ta duniya ta zama mai cikakken ‘yanci a cikin dukkanin ayyukanta.

Ya ce babban abin da yake da muhimmanci a kowane lokaci shi ne hukumar ta zama mai bin ka’idojin da aka kafata a kai, ba tare da saka siyasa a cikin ayyukanta ba, kamar yadda kuma bai kamata ta tasirantu da duk wani abu da ya saba wa ka’idojin aikinta ba.

Wannan na zuwa ‘yan kwanaki bayan fitar da wani bayani na sirri ne da Iran ta aike wa hukumar, wanda ya fita tun kafin alkalan hukumar su samu bayanin, wanda kuma hakan babban laifi ne a mahanga ta dokar kasa da kasa.

Baya ga haka ma Iran tana zargin hukumar da bayar da sunayen masana masu aiki a cibiyoyinta na nukiliya ga makiyanta, wanda hakan ke baiwa makiyan kasar ta Iran damar yin kisan gilla a kan masanan kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!