Yedioth Ahronoth: Ben Salman Na Da Hannu Wajen Sanya Morocco Ta Kulla Alaka da Isra’ila

Kafofin yada
labaran Isra’ila sun bayar da rahototanni kan cewa, yarima mai jiran gadon
Saudiyya Muhamamd Bin Salman ya takara rawa wajen kulla alaka tsakanin Morocco
da Isra’ila.
Jaridar Isra’ila ta
Yedioth Ahronoth ta bayar da rahoton cewa, tun kimanin shekara guda da
ta gabata, aka shirya gudanar da wata tattaunawa tsakanin sarkin Morocco, da
firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma sakataren harkokin wajen
Amurka gami da yariman Saudiyya ami jiran gado Muhammad Bin Salman.
Jaridar ta ce
saboda bayanai sun fita ga manema labarai dangane da wannan gazawa tun kafin
lokacinta, wannan yasa ganawar ba ta yiwuwa ba, saboda sarkin Morocco na tsoron
abin da hakan zai iya haifar masa a cikin gida.
Jaridar ta ce ko
shakka babu Muhammad Bin salman mai jiran gadon sarautar Saudiyya shi ne ya yi
tasiri a kan sarkin Morocco wajen sanar da kulla alaka da Isar’ila.
Ta kara da cewa
wanann ba shi ne na karshe ba, domin kuwa akwai wasu kasashen da Saudiyya take
da tasiri a kansu wadanda za su biyo baya, baya ga UAE, Bahrain da kuma Sudan gami da Morocco, daga ciki akwai kasashe irin su Oman, Indonesia,
Pakistan, Jibouti da makamantansu.
Manufar hakan dai ita ce sanya kasashen musulmi da na larabawa su sanar da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila, kafin daga bisa ita kuma masarautar saudiyya ta fito ta bayyana sanarwata, domin sauran kasashe su zame mata kariya daga martani da sukar da za ta fuskata daga al’ummomin musulmi kan haka.
015