‘Yan Bindiga Sun Sace Dalibai Masu Yawa A Makarantar Kwana A Jihar Katsina Najeriya

Wasu rahotanni
da ke fitowa daga jihar Katsina a Najeriya sun bayyana cewa, a daren jiya ne 'yan
bindiga suka kaddamar da hari a makarantar sakandaren maza ta GSSS da ke garin Kankara,
inda suka tarwatsa dalibai, suka kuma kame wasu masu yawa suka yi awon gaba da su.
Rotanni sun tabbatar da cewa, ‘yan
bindigar sun kai harin da kimanin karfe 9: 40 na daren jiya Juma’a, inda suka
yi harbe-harbe da bindigogin AK 47, lamarin da ya firgita dalibai, wasu daga
cikinsu suka fantsama cikin daji, yayin da kuma ‘yan bindigar suka kame wasu
daga cikinsu suka yi awon gaba da su.
Wasu bayanai na cewa wasu daga
cikin daliban da suka fantsama a cikin daji sun dawo, yayin da kuma wasu ahr
yanzu ba a san makomarsu ba.
Jami’an ‘yan sanda sun ce an yi
musayar wuta tsakanin ‘yan bindigar da kuma wasu ‘yan sanda da suke kan aiki a
lokacin, inda daya daga cikin ‘yan sanda ya samu raunuka.
Sai dai wasu daga cikin mutanen garin sun sheda cewa, tun yammacin jiya Juma’a suka samu bayani kan cewa ‘yan bindigar za su kawo hari, kuma an sanar da jami’an tsaro kan hakan, amma babu wani mataki da aka dauka na tsaro domin kare daliban.