An zartar Da Hukuncin Kisa Akan Ruhullah Zam A Iran

2020-12-12 09:43:07
 An zartar Da Hukuncin Kisa Akan Ruhullah Zam A Iran

Sa’o’i kadan da su ka gabata ne aka sanar da zartar da hukuncin kisa akan Ruhullah Zam wanda ya jagoranci wata kafa ta Telegrem da ta rika watsa labaran karya da tunzura mutane

Dakarun kare juyin musulunci na Iran ne su ka kamo Zam, bayan da ya dauki lokaci yana yana amfani da kafar telegram wajen watsa labarun karya akan Iran da kuma yi wa kungiyoyin leken asirin waje aiki.

Ruhullah Zam ya kasance a kasar Faransa inda daga can yake aiwatar da ayyukansa na batunci ga juyin musulunci, sai dai dakarun kare juyi sun yi nasarar dawo da shi gida inda ya fuskanci shari’a.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!