Wilayati: Kulla Alaka A Tsakanin Moroko Da HKI Cin Amanar Duniyar Musulunci Ne

2020-12-12 09:33:31
Wilayati: Kulla Alaka A Tsakanin Moroko Da HKI Cin Amanar Duniyar Musulunci Ne

Wilayati: Kulla Alaka A Tsakanin Moroko Da HKI Cin Amanar Duniyar Musulunci Ne

Shugaban Cibiyar Farkawar Musulunci ta Iran Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa; Dama tun shekaru 42 da su ka gabata, a lokacin sarki Hassan na 2, bayan da Masar da HKI su ka kulla yarjejeniyar Camp David, Moroko ta bayyana cewa a shirye take ta kulla alaka da HKI, kuma ta yi hakan a 1995 har zuwa 2000. Sai dai bayan barkaewar boren Intifada na Palasdinawa, Morokon ta katse alakarta da HKI.”

Ali Akbar Wilayati ya ci gaba da cewa; Abin takaici ne yanzu ace Morokon ta sake kulla alakar da ‘yan Sahayoniya,sannan kuma manyan ‘yan sahayoniya sun rika kai mata ziyara daga cikinsu hadda Ishaq Rabin da Sham’un Periz, sun kuma ci gaba da hulda a asirce.

A cikin wannan shekarar ta 2020, kasashen larabawan yankin tekun pasha da su ka hada Behrain, HDL sun sanar da kulla alaka da HKI.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!