Iran Da Afghanistan Sun Kaddamar Da Layin Jirgin Kasa Na Hadin Guiwa Da Zai Hade Kasashen Biyu

2020-12-10 22:49:00
Iran Da Afghanistan Sun Kaddamar Da Layin  Jirgin Kasa  Na Hadin Guiwa Da Zai Hade Kasashen Biyu

A yau Alhamis ce Hassan Rohani shugaban kasar Iran da takwaransa na kasar Afghanistan Ashraf Gani suka kaddamar da layin dogo da zai hade Gabashin Iran da Yammacin kasar ta Afghanistan, kuma dukkan shuwagabannin sun yi fata hakan zai kara daukaka harkokin kasuwanci tsakanin kasashen.

A nasa bangaren shugaban Iran Hassan Rohani ya fadi cewa: kasashen biyu a kowanne lokaci suna da kyakkyawar dangantaka tsakaninsu don haka aikin shimfida layin dogon zai kara taimaka wa wajen karfafa dankon zumunci tsakaninsu.

Daga karshe shi ma shugaban kasar na Aghanistan Ashraf Gani ya yi marhabin da wannan mataki mai cike da tarihi tare da bayyana shi a matsayin wani mataki babba da zai ciyar da tattalin arzikin kasashen guda biyu.

Layin dogon mai nisan kilo mita 225 ya kunshi bangarorin 4 ne wanda yanzu haka aka bude, yayin da kilo mita 78 na wannan aiki da ya hada da bangarorin biyu yana bangaren kasar Iran ne yayin da sauran kuma yake cikin kasar Afghanistan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!