Jam’iyyar Adawa A Ghana Ta yi Watsi Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da Aka Sanar

2020-12-10 22:43:46
Jam’iyyar Adawa  A Ghana Ta yi Watsi Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Da Aka Sanar

Sakamakon Zaben shugaban kasa da na ’yan majalisu da Hukumar zabe ta kasar Ghana ta fitar ya nuna cewa shugaban kasar mai ci a yanzu Nan Akufo –Addo ya doke tsohon abokin hamayyarsa John Mahama inda ya lashe zabe a karo na biyu.

Sai dai dan takarar neman shugabancin kasar karkashin jami’iyar Adawa ta NDC John Mahama ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da na yan majalisar da aka sanar, in da ya yi zargin yin magudi da harigidon kuri’u.

Nan Akofo Addo shugaban kasar Ghana mai ci a yanzu ya lashe zaben ne da kaso 51.50 cikin dari na dukkan kuri’un da aka kada yayin da a abokin hammayarsa John Mahama ya sami kaso 47.36 cikin dari.

Sai dai duk da matsalar cutar korona da ake fama da ita sama da mutane miliyan 13 ne suka fito, wato kaso 79 cikin dari na wadanda suka yi rijistar sunayensu.


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!