Jamal Khidri Ya Caccaki M D D Kan Kasa Tabuka Komai Wajen Kawo Karshen Killace Yankin Gaza Da HKI Take yi
2020-12-10 22:41:17

A wani taron manema labarai da shugaban kwamitin dake fada da ci gaba da killace zirin Gaza ya yi Jamal Khidri ya fadi cewa shekaru 14 kenan HKi na ci gaba da killace yankin gaza amma MDD da sauran masu fada aji na duniya sun kasa yin komai a kai, da hakan ya ci karo da taken kare hakokin dan Adama da MDD take rerawa.
Har ila yau ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su
gaggauta kawo karshen killace zirin Gaza ta hanyar matsin lamba kan HKI,kana ya baukaci da su dawo daga daukar matakin yin Allah wadai, su dauki
mataki a aikatace ne kan HKI.
Abin takaici duk da cewa killacewar na cutar da sama da Palasdinawa
sama da miliyan biyu amma babu abin da
ake yi a kasa.
Shi dai wannan jami’in ya fadi haka ne sa’ilin da yake ishara
game da rahoton baya bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar game da asarar kudi har dala biliyan 16
sakamakon killace yankin Gaza da HKI ta yi.
Daga karshe ya nuna cewa yankin Gaza yana fuskantar killacewa mafi tsawo a wannan zamani.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!