Iran ce Ta 29 A Duniya A Matsayin Da Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya Ke Fitarwa A Duk Wata

2020-12-10 22:38:50
Iran ce Ta  29 A Duniya A Matsayin Da Hukumar Kwallon Kafa Ta Duniya Ke Fitarwa A Duk Wata

A ci gaba da sakamakon da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA take fitarwa a duk wata , a wannan karon sakamakon na karshen shekara ya nuna cewa Iran ta kare a matsayi na 29 a a duniya ta 2 a Asia bayan kasar Japan , bayan da ta samu maki 1082 a dukkan wasannin da ta buga na kasa da kasa a shekara ta 2019, kuma shi ne adadi mafi yawa da hukumar ta FIFA ta fitar tun daga shekara ta 1993.

Kasar Belgium dai har yanzu ita ce gaba da kasancewa akan gaba a matsayin da hukumar ta FIFA take fitarwa a tsawon shekaru 3 a jere.

Haka zalika kasar faransa ita ce ta 2 sai Brazil a matsayin ta 3 yayin da Ingila ta ci gaba da kasancewa ta 4 , sai dai canjin da aka samu kawai shi ne kasart Portugal ta koma ta biyar a duniya.

Hukumar kallon kafa ta duniya FIFA za ta sake fitar da wani sabon matakin ne na matsayin kowace kasa a duniya nan da 18 ga watan Fabarerun shekara ta 2021.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!