Najeriya: Gwamnonin APC Ba Su Amince Da Gayyatar Buhari A Gaban Majalisa Ba

2020-12-10 14:31:16
Najeriya: Gwamnonin APC Ba Su Amince Da Gayyatar Buhari A Gaban Majalisa Ba

Gwamnonin APC a Najeriya sun bayyana cewa ba su amince shugaba Buhari ya bayyana a gaban majalisar Kasa ba, bayan da ya sanar cewa zai bayyana a gaban majalisar a yau Alhamis.

Jaridar Premium Times ta bayar da rahoton cewa, gwamnonin APC sun bayyana cewa, idan har ‘yan majalisar tarayya za su rika yin kiranye ga shugaban kasa domin ya bayyana gabansu, to ‘yan majalisun jihohi ma za su samu damar da za su rika aikewa da kiranye ga gwamnoni, domin su bayyana gaban majalisa.

Wannan yasa dukkanin gwamnonin bakinsu ya zo daya, kan kin amincewa da bayyanar shugaban kasa Muhammadu Buharia gaban majlisar dokokin Najeriya, domin bayar da bahasi kan halin da ake ciki dangane da batun tsaro a kasar.

Haka nan kuma gwamnonin na APC sun ce sun bankado wani shiri da mambobin jam’iyyun adawa ke shi a majalisar, na neman su kunyata shugaba Buhari idan ya bayyana a gaban su.

Rahoton ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisa sun soki matsayar da gwamnonin na APC suka dauka, inda suka bayyana cewa hana shugaban kasa bayyana a gaban majalisa bai dace ba, musamman ma ganin cewa shi da kansa ya bayar da hadin kai kan hakan, kuma ya amsa kiranyen da aka yi masa, a kan cewa zai hallara a gaban majaliasr kamar yadda aka bukata.

Masana shari’a a Najeriya na cewa, sashe na 88 da kuma na 89 na kundin tsarin mulkin kasar, ya baiwa ‘yan majalisar dokoki damar yin kiranye ga kowane irin jami’i na hukuma a kasar domin ya bayyana gabansu, da hakan ya hada har da shugaban kasa, sabanin abin da ministan shari’a na kasar Abubakar Malami ya fada.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!