Amurka: Kotu Ta Bukaci CIA Da Ta Bayar Da Bayanan Da Take Da Su Kan Kisan Khashoggi

Wata kotu a Amurka ta
bukaci hukumar leken asiri ta kasar CIA da ta bayar da cikakken rahoton da take
da shi dangane da kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya Jamal Khashoggi
a cikin ofishin jakadancin kasar ta Saudiyya a Turkiya.
Bisa ga rahoton da kamfanin
dillancin labaran Bloomberga na Amurka ya bayar, Paul Engelmeier alkalin wata
kotu a birnin New York na Amurka, ya bukaci hukumar CIA da ta bayar da cikakken
rahoto kan kisan gillar da aka yi wa dan jaridar Saudiyya Jamala Khashoggi.
Alkalin ya ce babu bukatar gabatar
da wasu dalilai kafin gabar da wannan bukata, domin kuwa hukumar leken asirin
Amurka CIA tana da cikakkiyar masaniya kan hakikanin abin da ya faru na kisan
gillar da aka yi wa Khashoggi a cikin ofishin jakadanin Saudiyya a Istanbul.
Ya kara da cewa, shugaban kasar
Amurka Donald Trump da kansa ya fadi a zantawarsa da tashar talabijin ta Fox
News a cikin watan Nuwamban 2018 kan cewa, Amurka tana da hoton bidiyo na kisan
Khashoggi.
Alkalin ya ce bisa ikirarin da
shugaban Amurka ya yi da kansa, da kuma shugaban hukumar CIA Gina Haspel kan
cewa suna cikakkun bayanai kan yadda aka kashe Khashoggi, wannan ya isa hujja
kan cewa CIA tana da bayani kana bin da ya faru, kuma kotu na bukatar wadannan
bayanai.
A cikin watan Oktoban 2018 ne jami’an tsaron kasar Saudiyya da suka hada har da wasu daga cikin masu tsaron lafiyar Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, suka yi wa Jamal Khashoggi kisan gilla, ta hanyar yi masa gunduwa-gunduwa tare da narkar da namansa da sanadarai na acid.
015