​Kaftin Din Manchester United Ya Ce Akwai Bukatar Warware Matsalolin Cikin Gida Na Kungiyar

2020-12-10 14:10:08
​Kaftin Din Manchester United Ya Ce Akwai Bukatar Warware Matsalolin Cikin Gida Na Kungiyar

Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasar Burtaniya Harry Maguire, ya bayyana cewa dole shugabannin kungiyar da ‘yan wasa su koma su tattauna su yi shawara da juna, domin ganin sun samu nasara a wasanni na gaba sannan su nemo hanyar shawo kan matsalolin da suka addabi kungiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai ta yi rashin nasara a wasan karshe da ta buga a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, wanda aka buga a gidan mai masaukin baki RB Leipzig a kasar Jamus a ranar Talata, inda aka ci Manchester United 3 – 2.

A cikin mintuna na 13 ne da fara wasan aka zurawa Manchester United kwallo biyu a cikin raga, ina Angelino da kuma Amadou Haidara suka fara saka kwalle na farko, sai kuma a mintuna na 69 bayan dawowa hutun rabin lokaci, Justin Kluivert ya kara kwallo ta uku a ragar Manchester United.

A minti na 80 wato saura mintuna 10 kayyadadden lokacin wasan ya kare, Man United ta fara saka kwallo ta farko, wadda Bruno Fernandes ya saka ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida, mintuna biyu bayan haka kuma dan wasa Paul Pogba ya sake narka wa Man United kwallo ta biyu, amma har aka tashi wasan ba ta iya farke kwalle uku da aka zura mata ba.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!