Iran Ta Kakaba Wa Jakadan Amurka A Yemen Takunkumi

2020-12-10 09:49:28
Iran Ta Kakaba Wa Jakadan Amurka A Yemen Takunkumi

Jamhuriyar Musulinci Ta Iran, ta sanar da kakaba takunkumi kan jakadan Amurka a kasar Yemen, wanda ta zarga da hannu a bala’in da dake ci gaba da faruwa a kasar Yemen.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran, ta fitar, a jiya Laraba, ta ce ta sanya sunan Christopher Henzel, wakilin Amurka a kasar te Yemen, dake jerin mutanen data kakaba wa takunkumi saboda hannun da yake da shi wajen ruguza kasar Yemen, da kisan wadanda basu ji basu gani ba, da kuma taimakon kawancen dake yaki a kasar ta Yemen.

Iran ta ce duk wadanan laifufuka sun sabawa dokokin kasa da kasa da hakkin dan adam.

Wannan matakin na Iran dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin shugaba Trump mai barin gado, ta sanya wa jakadan Iran a kasar Yemen takunkumi.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!