Tigray : MDD Da Habasha Sun Cimma Sabuwar Yarjejeniya

2020-12-10 09:46:19
Tigray : MDD Da Habasha Sun Cimma Sabuwar Yarjejeniya

Majalisar Dinkin Duniya, da kuma kasar Habasha, sun cimma wata sabuwar yarjejeniya kan batun yankin Tigray, domin shirya yadda za’a isar da kayan tallafi ga jama’ar yankin, kamar yadda babban sakataren MDD, Antonio Guteress ya sanar.

Ganin cewa bamu samu aiwatar da yarjejeniyar farko ba, yanzu mun cimma wata ta biyu, data kunshi tawagar hadin guiwa ta MDD da kuma gwamnatin Habasha domin duba ababen da jama’a ke bukata a yankin na Tigray, inji shugaban kwamitin kungiyar tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat.

Wannan matsaya da muka cimma a yanzu, zata bada damar shiga lungu da tsako na yankin domin gudanar da ayyukan jin kai ba tare da nuna bangaranci ba a cewa MDD.

Wannan ba shi ne karon farko ba da MDD, da kasar ta Habasha, ke cimma irin wannan yarjejeniya ba, don kuwa ko a mako guda da ya gabata sun cimma irinta wacce ta tanadi kai agaji ga al’ummar yankin.

Yankin Tigray dai ya fada cikin halin rashin tabas, tun bayan da firaministan Habasha, ya aike da sojojin tarrayya a yankin a ranar 4 ga watan Nuwamba da ya gabata domin fatatakar jagororin yankin na kungiyar TPLF.

Mutane kimanin 50,000 ne suka kauracewa rikici a yankin inda suke kwarara zuwa cikin makobciyar kasar Sudan.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!