Najeriya Ta Musanta Zargin Amurka Game Da Keta Hakkin Bin Addinai

2020-12-10 09:41:54
Najeriya Ta Musanta Zargin Amurka Game Da Keta Hakkin Bin Addinai

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar da wata sanarwa dake musanta zargin da Amurka ta yi wa kasar, na keta hakkokin al’ummunta na bin addinin da suke so.

Kamfanin dillancin labarai na na China, Xinhua ya rawaito daga wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta fitar na cewa za ta gaggauta tattaunawa da mahukuntan Amurka game da wannan al’amari.

Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen Najeriyar ta ce zargin na Amurka yana da ban mamaki, duba da cewa Najeriya ba kasa ce dake bin wani addini guda daya ba, kuma mahukuntan kasar na martaba dukkanin ‘yancin bin addinai da ‘yan kasar suka zaba da kan su.

A ranar Talata data gabata ce, Amurka ta fitar da rahoton ta na shekara shekara kan batun tauye yancin yin addinin da mutum ya fahimta, inda ta saka Najeriya a cikin jerin kasashen da ta ce suna toye wannan hakkin ga al’ummunsu.

Saidai Amurka bata bayyana takamaimai abunda ta ke zargin Najeriyar da shi ba kan toye hakkin gudanar da addini.

Amma a wani rahotonta data wallafa a baya, gwamnatin Amurka, ta nuna damuwa kan yadda mahukuntan na Najeriya ke amfani da karfin tsiya wajen murkushe ayyukan mabiya mazahabar shi’a, wanda ya kai har ga haramta kungiyarsu, wanda bangarori daban daban na Najeriyar, suka danganta da babbar barazana ga yancin gudanar da addini a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!