An Fara Gwajin Riga-Kafin Cutar Corona Kirar Iran Akan Mutane

2020-12-09 19:42:19
 An Fara Gwajin Riga-Kafin Cutar Corona Kirar Iran Akan Mutane

Kakakin hukumar abinci da magunguna ta Iran Kiyanush Jihanpor ya sanar a yau Laraba cewa; An fara gwajin riga-kafin cutar ta corona akan mutane da su ka sadaukar da kawukansu, kuma anan gaba za a yi wata sanarwar idan bukatar hakan ta taso.

Kiyanoush ya kara da cewa; Kamfanin da ya samar da riga-kafin ya sami izini daga hukumar abinci da magani ta kasa, kuma mutanen da aka yi wa riga-kafin na farko ana bibiyar halin da suke ciki na tsawon wata daya.

Kakakin hukumar abinci da magani na Iran din ya kuma bayyana cewa; Mutanen da aka yi gwajin na farko shekarunsu suna tsakanin shekaru 18 zuwa 50, kuma wadanda ba su dauke da wasu cutuka ne masu rikitarwa ko cutar corona.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!