Allah Ya Yi Wa Tsohon Alkalin Alkalan Iran Muhammad Yazdi Rasuwa

2020-12-09 19:35:49
Allah Ya Yi Wa Tsohon Alkalin Alkalan Iran Muhammad Yazdi Rasuwa

A yau Laraba ne Allah ya karbi rayin Muhammad Yazdi wanda tsohon alkalin alkalai ne na Iran kuma shugaban kungiyar malamai masu koyarwa a cibiyoyin ilimi na Hauza da ke birnin Qum.

Muahhamd Yazdi ya rike mukamin alkalin alkalan Iran ne daga tsakanin 1988 zuwa 2008, sannan kuma ya zama memba a majalisar kwararru mai zamabar jagoran juyin musulunci.

Wasu daga cikin makaman da ya rike da akwai babban sakataren majalisar koli ta cibiyar ilimi ta Hauza da kuma sakataren majalisar shawarar musulunci ta Iran sau biyu.

Har ila yau marigayin ya rubuta littafai da dama daga cikinsu akwai

“Ususul-Iman Fil Qur’an.

Nabzah Min Ma’ariful-Islamiyyah.

Ya rasu ne dai a yau Laraba yana dan shekaru 89.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!