Ghana : John Dramani Na Kan Gaba A Sakamakon Zaben Shugaba Kasa

2020-12-09 14:52:02
Ghana : John Dramani Na Kan Gaba A Sakamakon Zaben Shugaba Kasa

A kasar Ghana ana ci gaba da dakon sakamakon zaben shugabacin kasar da aka kada kuri’arsa a ranar Litini data gabata.

A halin da ake ciki dai babban dan takaran adawa na kasar, John Dramani Mahama ne ke kan gaba a zakamakon zaben.

Kafin hakan dai fadar shugaban kasar, ta fitar da wasu alkalumma na hasashe daga mazabu kashi 91% dake nuna cewa shugaban kasar mai barin gado Nana Afuko Addo, ya lashe zaben shugabancin kasar da kashi 52,25%, yayin da babban abokin hamayarsa M. Mahama ya samu kashi 46,44%, na yawan kuri’un da aka kada.

A wani labara kuma jam’iyyar NDC, mai adawa na cewa ta samu gagarimin rinjaye a majalisar dokokin kasar da kujeru 140.

Masu sanya ido dai a zaben sun ce sun gamsu da yadda zaben ya gudana.

Ana yi wa Ghana dai kallon misali na gari a tsarin demokuradiyya da kwanciyar hankali a yankin yammacin Afrika.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!