Burundi Ta Yaba Da Cire Ta Daga Jerin Kasashe Masu Matsalolin Siyasa

2020-12-09 14:40:16
Burundi Ta Yaba Da Cire Ta Daga Jerin Kasashe Masu Matsalolin Siyasa

Mahukunta a kasar Burundi, sun bayyana jin dadin su, bisa cire sunan kasar daga jerin kasashe masu matsalolin siyasa, da kwamitin sulhun MDD ke tattaunawa a kan su.

A ranar Juma’ar data gabata ne kwamitin sulhun MDDr, ya kawo karshen rahotannin da yake fitarwa, game da halin da kasar ke ciki a siyasance, tare da kira ga abokan huldarsa, da su ci gaba da tattaunawa don gane da sake ci gaba da tallafawa ci gaban kasar.

Da yake tsokaci game da hakan, cikin wata sanarwa da aka yada ta gidan radio da talabijin na kasar, kakakin gwamnatin Burundin M. Prosper Ntahorwamiye, ya ce wannan mataki ne mai cike da tarihi, wanda ke nuna amincewar da MDD ta yi, da irin muhimmin ci gaban da Burundi ta samu a sassa daban daban.

Gwamnatin Burundi dai ta sha nanata cewa, ba wata barazana da kasar ke haifarwa zaman lafiya da tsaron yankin, don haka ta ke kira ga kwamitin sulhun MDD da ya janye sunan ta, daga jerin kasashe masu irin wannan matsala.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!