​Dr. Rauhani: Iran Da Syria Suna Da Kyakkyawan Kawance A Bangarori Na Ci Gaban Al’ummominsu

2020-12-09 10:46:26
​Dr. Rauhani: Iran Da Syria Suna Da Kyakkyawan Kawance A Bangarori Na Ci Gaban Al’ummominsu

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mikdad da yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Iran, ya gana da manyan jami’an gwamnatin kasar ta Iran.

Shugaba Rauhani ya jaddada cewa babu gudu babu ja da baya dangane da ci gaba da kara karfafa alaka tsakanin Syria da Iran a fagage daban-daban da suke yin aiki tare, da hakan ya hada da batun yaki da ta’addanci.

Rauhani ya ce tsayin da jajurcewar al’ummar Syria gwamnatinsu da da sojojinsu da sauran al’ummar kasa, shi ne babban sirrin samu nasararsu a kan makircin da aka kullawa kasar da nufin rusa ta, saboda matsayarta ta kin amincewa da mika wuya ga manufofin kasashe masu girman kai da ‘yan korensu na yankin.

Kamar yadda kuma ya yi ishara da cewa kawayen Syria ba za su bar ta ita kadai ba a duk lokain da take bukatarsu, kamar yadda suka kasance tare da ita a fagen yaki da ta’addanci da ‘yan ta’adda a cikin kasarta.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!