​Buhari: Zan Bude Iyakokin Najeriya Nan Ba Da Jimawa Ba

2020-12-09 09:40:14
​Buhari: Zan Bude Iyakokin Najeriya Nan Ba Da Jimawa Ba

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, nan bad a jimawa ba Najeriya za ta bude iyakokinta da ta garkame na tsawon wasu ‘yan shekaru.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka ma shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya kudiri aniyar bude iyakoki nan bad a jimawa ba.

Buhari ya bayyana dalilin da suka sanya ya rufe iyakokin Najeriya da kasashe makwabtanta da cewa, hakan mataki ne na hana fasa kwabrin makamai da muggan kwayoyi, kuma kasashen da suke makwabtaka da Najeriya sun fahimci hakan a halin yanzu.

A jiya shugaba Buhari ya zanta da gwamnonin jihohin Najeriya baki daya, inda ya tabbatar musu da cewa gwamnatinsa ta yi matukar kokari na a zo a gani wajen tabbatar da tsaro, musamman a yankuna arewa maso gabashin Najeriya da kuma kudu maso kudancin kasar.

Haka nan kuma ya bukaci gwamnoni da su ci gaba da yin aiki tare da shugabannin al’umma, da suka hada da masu sarautun gargajiya, domin samun bayanai da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a kasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!