​Cristiano Ronaldo Ya Yi Raga-Raga Da Barcelona

2020-12-09 09:29:10
​Cristiano Ronaldo Ya Yi Raga-Raga Da Barcelona

A Wasannin cin kofin kwallon kafa na zakarun nahiyar turai, kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta kasar Italiya ta lallasa Barcelona ta kasar Spain da ci 3 – 0.

Wasan wanda ya gudana a jiya a filin wasanni na Barcelona a kasar Spian, fitattun ‘yan wasan nan biyu da suke bugawa wadannan kungiyoyin kwallon kafa wasa, wato Lionel Messi da kuma Cristiano Ronaldo sun hadu da juna, bayan share tsawon lokaci ba su yi arba da juna a filin wasa ba.

Ronaldo dai shi ne ya fara saka wa Juventus kwallo ta farko a cikin ragar Barcelona, bayan da ya buga wani bugun daga kai sai mai tsaron gida a cikin mintuna na 13 da fara wasan.

Sai kuma a mintuna na 20 dan wasan Juventus Weston Mckennie ya zura kwallo ta 2.

A mintuna na 52 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Cristiano Ronaldo ya saka kwallo ta uku a ragar Barcelona a wani bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma har aka tashi wasan Barcelona ba ta iya farkewa ba.

A halin yanzu dai Juvenstus ita kan gaba a runkunin G na gasar.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!