Maduro: An Yi Cikakken Shirin Kashe Ni A Ranar Zaben ‘Yan Majalisar Dokokin Venezuela

Shugaban kasar Venezuela Nicolar
Maduro ya bayyana cewa, an shirya yi masa kisan gilla a ranar Lahadin da ta
gabata,a lokacin gudanar da zaben ‘yan
majalisar dokokin kasar da ya gudana.
Shugaba Maduro ya bayyana hakan ne a
jiya a zantawarsa da manema labarai ta hanyar yanar gizo, inda ya tabbatar da
cewa an kammala dukkanin shirin yi masa kisan gilla a lokacin kada kuri’a, a
kan haka aka dauki matakai na canja wurin da zai jefa kuri’a.
Maduro ya ce maganar da yake yi ba
zargi ba ne ko shaci fadi, magana ce mai tushe, kuma sun samu dukkanin bayanan
ne daga majiyoyi na hukumar leken asirin kasar Colombia, da suka tabbatar musu
da cewa an shirya kisan ne a cikin kasar ta Colombia, tare da umarnin shugaban
kasar ta Colombia.
Ya ce bisa kokarin bangarorin leken
asiri na kasar Venezuela, sun iya gano dukkanin abin da aka shirya ta wasu
hanyoyi, kuma sun dauki matakan da suka dace a kan hakan.
A lokutan baya dai an yi shirin
kashe shugaba Maduro a lokacin taron ranar kasa, inda aka turo wani jirgi maras
matuki da yake dauke da bama-bama, wanda ya tunkari taron da Maduro ke halarta,
amma jirgin ya tarwatse a sama kafin isa kan shugaba Maduro, wanda shi ma
Venezuela ta dora alhakin hakan a kan Amurka da Colombia.
015