Iran: Duniya Za Ta Fi Zama Lafiya Idan Babu Haramtacciyar Kasar Isra’ila

2020-12-08 22:09:07
Iran: Duniya Za Ta Fi Zama Lafiya Idan Babu Haramtacciyar Kasar Isra’ila

A wani taron da manyan jami’an gwamnatin kasar Iran suka gudanar tsakaninsu da sabon ministan harkokin wajen kasar Siriya Faisal Mikdad dake ziyarar aiki ta farko a irinta a kasar tun bayan kama aiki, sun tattauna game da bakar siyasar da Isra'ila ta ke aiwatarwa a yankin gaba ta tsakiya, kana sun Jaddada cewa babu Isra'ila duniya za ta fi zama lafiya da kwanciyar hankali.

A nasa bangaren Sakataren majalisar koli ta tsaro ta kasar Iran Ali Shamkhani ya fadi a wajen taron cewa babbar manufar kasancewa kasar Amurka a siriya shi ne ci gaba da tatsar arzikin man fetur din kasashen larabawa da kuma kare Isra'ila da karfafa kungiyar yan ta’adda ta Da’esh don haka dole ne a kawo karshen ci gaba da zaman babban shedani a yankin.

Ya kara da cewa wanzuwar Isra'ila ya doru ne akan ci gaba da take hakkin dan adama da ayyukan ta’adanci don haka ya zama wajibi hukumomi masu fada aji na duniya su mike domin kawo karshen zubda jin da gwamnatin Yahudawan Sahubiya take yi .

Daga karshe ya tabbatar da cewa Iran ba za ta kyale kasar Siriya ta yaki yan ta’adda ita kadai ba.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!