An Raba Jadawalin Shiga Kofin Duniya Na Yankin Nahiyar Turai

2020-12-08 21:42:25
An Raba Jadawalin Shiga Kofin Duniya Na Yankin Nahiyar Turai

Kasar Ingila za ta fafata da Poland a rukuni na tara a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara ta 2022 da kasar Qatar za ta dauki bakunci. Kasashen Hungary da Albania da Andorra da kuma San Marino ne ke rukunin daya da kasar ta Ingila.

Scotland za ta kece raini da Denmark da Austria da Israela da tsibirin Faroe da kuma Moldova a rukuni na shida. Kuma Za a fara wasannin ne daga watan Maris zuwa Nuwambar shekara ta 2021 mai zuwa,

Saboda irin yanayi na zafi a kasar Qatar, za’a gudanar da gasar cin kofin duniya din ne da kasar Qatar za ta karbi bakunci daga 21 ga watan Nuwamba zuwa 18 ga Disambar 2022. Hakan zai sa gasar ta zama ta farko da za a gudanar da ita sabanin watanni Mayu ko Yuni ko kuma Yuli da aka saba.

Kuma za a gudanar da wasannin a kwana 28, da ake sa ran kasashe 32 za su kece raini a filaye takwas a birane biyar da za su karbi bakuncin gasar.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!