Ana Ci Gaba Da Kidaya Kuri’un Da Aka Kada A Zaben Shugaban Kasa Da Na “Yan Majalisu A Kasar Ghana

2020-12-08 21:36:06
Ana Ci Gaba Da Kidaya Kuri’un Da Aka Kada A Zaben Shugaban Kasa Da Na “Yan Majalisu A Kasar  Ghana

Duk da yake cewa an gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majilisu cikin kwanciyar hankali a kasar ta Ghana a jiya Litinin, amma jami’an tsaro sun dauki tsauraran mataken tsaro a babban birnin kasar Accra, bayan da wasu ‘yan kasar suka fara murna game da nasarar da suke ganin dan takararsu ya samu.

Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar shugabancin kasar kuma mai ci a yanzu Nana Akufo Ado shi ne ke kan gaba ya zuwa yanzu, sai dai dan takarar shugabancin kasar bangaren jami’iyar NDC mai adawa John Mahama ya yi watsi da sakamakon da aka fara fitarwa inda ta yi zargin yi masa magudi.

Sau 7 kasar Ghana tana miki mulki ga jam’iyar da ta lashe zabe cikin lumana daga lokacin da ta koma turbar mulkin Demukuradiya.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!