Gwamnatin Nigeria Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa N162.44 Kan Kowacce Lita

2020-12-08 21:33:10
Gwamnatin Nigeria Ta Rage Farashin Man Fetur Zuwa N162.44 Kan Kowacce Lita

A wata hira da Ministan Kwadago na Nigeria Chris Ngige ya yi da manema labarai a daren jiya Litinin jim kadan bayan kammala zama da ya yi da kungiyoyin kwadago na kasar ya fadi cewa: gwamnatin kasar ta yanke shawarar rage farashin man fetur daga N168 zuwa N162.44 kan kowace lita don rage tsadar rayuwa da al’umma ke ciki.

Yanzu haka dai ana sayar da man ne a kan N168, kuma hakan ya biyo bayan matakin da 'yan kasuwa suka dauka na kara farashin daga N147.67 zuwa N155.17 a watan Nuwamba da ya gabata.

Har ila yau Chris Ngige ya kara da cewa an kafa wani kwamitin bincike da zai daidaita farashin man, ya ce Tattaunawar da suka yi tsakaninsu da kungiyoyin kwadagon, ta yi ma’ana sosai. shi ma babban kamfanin mai na NNPC, da 'yan kasuwa sun amince da rage farashin man da N5, kuma zai fara aiki nan daga ranar Litinin mai zuwa.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!