Shamkhani: Iran Da Syria Za Su Ci Gaba Da Yin Aiki Tare A Dukkanin Bangarori

2020-12-08 15:27:06
Shamkhani: Iran Da Syria Za Su Ci Gaba Da Yin Aiki Tare A Dukkanin Bangarori

Babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya bayyana cewa, Syria da Iran za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a ganawar da ta gudana a yau tsakanin ministan harkokin wajen kasar Syria Faisal Mikdad da kuma babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani, an tattauna batutuwa da suk shafi alaka tsakanin kasashen biyu ta fuskanci tsaro.

Babban sakataren majalisar tsaron kasa a Iran Admiral Ali Shamkhani ya jaddada cewa, Syria da Iran za su ci gaba da yin aiki tare a dukkanin bangarori musamman a bangaren yaki da ta’addanci.

Ya ci gaba da cewa Iran ta kasance tare da Syria a yaki da ta’addanci tsawon shekaru 10, kuma za su ci gaba da yin aiki a wanna bangarea tare.

Shi ma nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar ta Syria Faisal Mikdad ya jaddad godiyar kasarsa ga Iran, kan sadukarwar da ta yi wajen taimakon Syria a dukkanin bangarori

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!